Da ya sace Mahaifinsa,ya karbi fansar Naira Miliyan 1 | isyaku.com

Wani abin mamaki ya faru a garin Ibadan inda wani yaro dan shekara 20 ya shaida wa manema labarai cewa shine wanda ya shirya yadda aka sace mahaifinsa mai suna Alh.Aliyu Babatunde daga garin Igboora kuma aka tsare shi har kwanaki uku a mabuyarsu kafin aka sake shi bayan iyalinsa sun biya fansar naira miliyan daya ga wadanda suka saceshi.

Yaron mai suna Ibrahim Aliyu Babatunde ya shaida wa yansanda a Eleyiele a Ibadan cewa shi da wasu yaran ne suka aikata wannan aiki wadanda suka hada da  Babuga Salihu (20), Aura Sands (20), da Amuda Yusufu (19).

Ibrahim wanda da ne ga Alh.Aliyu ya shaida wa 'yan Jarida cewa ya aikata wannan aikin ne saboda mahaifinsa baya kulawa da jindadin yaransa."Muna da yawa a gidanmu,Mahaifina yana da Mata da yawa,saboda haka baya kulawa da harkokinmu wanda ya zama wajibi mu kula da kanmu.Wannan shine dalilin da yasa na yi tunanin cewa in tsara yadda zan zabbari kudi daga gurin Mahaifina saboda in kula da kaina".


@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka aiko mana rahotu ? ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN