'Yan bindiga sun kashe mataimakin kwamishinan 'yan sanda

Wasu da ake zaton 'yan bindiga dadi ne sun harbe wani babban hafsan dansanda har lahira mai mukamin mataimakin kwamishinan 'yan sanda. ACP Usman Ndanbabo shine kwamdan sashen rundunar 'yan sanda na Ughelli a jihar Delta kafin rasuwar sa a ranar 8,Mayu 2017.

Majiyar mu ta shaida mana cewa Marigayin ya lura cewa wata mota tana biye da shi a yayin da yake dawowa gida a cikin motar sa Nissan  SUV a randabawal da ke gefen fadar basarake Ovie na Ughelli sai yayi kokarin tsarewa amma maharan suka buda mashi wuta inda suka harbe shi a baya da cikinsa.

An garzaya da Usman Ndanbabo wasu Asibitoci domin samun taimakon gaggawa amma sun baiyana cewa basu da ingantattun kayan aiki da zasu yi amfani wajen taimaka masa.Daga bisani an garzaya da shi wani Asibiti da ba'a bayyana ba inda Allah yayi mashi cikawa.

Bayanai sun nuna cewa wannan shine karo na biyu da aka yi yunkuri akan rayuwarsa tun lokacin da ya kama aiki a wannan yankin.ACP Ndanbabo ya jagoranci 'yan sanda 60 suka fitar da wasu da ake zargin Filani ne da suka shiga wata gona da karfi kuma suka yi kaka gida a ciki.

@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN