Rahotanni daga birnin Calabar na
jihar Cross River na cewa an tafka wani fada
tsakanin 'yan sanda da sojojin ruwan Najeriya, inda ake tunanun an yi
asarar rayuka da wasu da dama kuma sun jikkata.
Amma rundunar ba ta yi karin bayani kan asarar rayuka ko jikkata ba.
Wasu rahotanni sun ce rikicin ya fara ne a yayin da wani dan sanda ya yi kokarin tsayar da motar sojojin, wadda ta ki bin umarnin danjar bayar da hannu.
Fadan ya yi kamari ne yayin da wasu manyan jami'ai suka yi kokarin sasantawa, amma daga bisani sai al'amura suka rincabe.
Kafar yada labarai ta Premium Times ta ruwaito cewa wani ganau ya shaida mata cewa daga nan sai sojojin suka shiga cikin ofishin 'yan sandan na Akim inda suka fara harbe-harbe suka kuma kona ofishin.
@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka aiko mana rahotu ? ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com
Wannan labarin ya fara bayyana a shafin BBC
Tags:
LABARI