• Labaran yau

  Majalisar Dokoki ta jihar Kano ta jingine bincike akan Masarautar Kano | isyaku.com

  Majalisar Dokoki ta jihar Kano ta jingine binciken da take yi akan Masarautar Kano karkashin Sarki Sanusi Lamido Sanusi na 2 akan zargin aikata ba daidai ba.

  Wannan ya biyo bayan shiga tsakani da wasu fitattun 'yan Najeriya suka yi ne inda suka roki Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya jingine binciken saboda tabbatar da dorewan zaman lafiya a kasar Kano.

  Kakakin Majalisar Dokiki na jihar Kano Alh.Kabir Alhassan Rurum ya shaida wa Majalisar yau Litinin cewa Gwamna Ganduje ya rubuto wasika zuwa Majalisar inda yake bukatar a jingine bincike da Majalisar ke yi akan Masarautar ta Kano.

  Kakakin ya kara da cewa Ganduje ya lissafa wasu fitattun 'yan Najeriya a cikin wasikar wadanda suka hada da Mukaddashin shugugan kasa Yemi Osinbajo,tsohon shugaban kasa Ibrahim Babangida da Abdulsalami Abubakar,da Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar,Aliko Dangote,Aminu Dantata da sauran su.

  Sahara Reporters ta ruwaito cewa wasikar ta Ganduje ta yi nuni da kalaman Sarki Sanusi a wani taro a Kaduna inda Sarki Sanusi ya amshi kuskuren sa kuma ya roki gafara ga Gwamnatin jihar Kano.

  A bisa wannan dalili Ganduje ya nemi Majalisar Dokoki ta jihar Kano ta jingine bincike da take akan Masarautar wadda 'yan Majalisar suka amince da gaggarumin rinjaye.


  @isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Majalisar Dokoki ta jihar Kano ta jingine bincike akan Masarautar Kano | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama