Aisha Buhari: Mijina ba ya rashin lafiyar da za ta sa shi fita kasar waje

A dai-dai lokacin da mutane suke ta cece-kuce game da lafiyar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kan ya fita kasar waje don neman magani, mai dakin shugaban Aisha Muhammadu Buhari ta bayyana wa duniya cewa, babu bukatar shugaban ya sake fita wata kasa don neman magani.
A wani sako da ta fitar ta shafin Twitter wanda mai magana da yawunta ya tabbatar, Aisha Buhari ta ce, kamar yadda kowa ya gani shugaban na Najeriya na samun sauki kuma a ranar talatar nan ma ya gana da ministan Shari’a inda ya ke ci gaba da gudanar da aiyukansa na Office.
Wannan kalamin ata ya zo kwana 1 bayan jagoran jam’iyyar APC na Najeriya Bisi Akande ya bayyana damuwarsa game da halin da shugaba Buhari ya ke ciki inda ya ce, rashin lafiyar ta Buhari na shafar yadda ake jagorantar Najeriya.
Akande ya zargi wasu mutane da ke kewaye da shugaban kasar da cewa, suna kokarin karya doka da oda.

@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb

Aisha Buhari: Mijina ba ya rashin lafiyar da za ta sa shi fita kasar waje ya fara bayyana a TRT

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN