'Yan kasar Gambiya sun fara kosa wa da gwamnatin Barrow mai kwanaki 100

A dai-dai lokacin da shugaban kasar Gambiya Adama Barrow ya cika shekaru 100 a kan mulki, jama’ar kasar na korafi game da yadda babu wani abu da aka fara yi na magance matsalolin da jama’a suke fuskanta.
Masu sukar gwamnatin Barrow na cewa, shugaban ba shi da wani tsari a kasa na kawo ci gaba tare da magance matsalolin Gambiya bayan mulkin danniya na tsawon shekaru 22 da Yahya Jammeh ya yi.
Wani mai nazari kan al’amuran siyasa a jami’ar Gambiya Isma’ila Ceesay ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa, sabuwar gwamnatin ta gaza a cikin kwanaki 100 inda ba da iya cka wani alkawari da ta yi ba.
Ya ce, matsalar ita ce, gwamnatin ba ta da tsari mai kyau. Kawai da ma burinsu shi ne su kawar da Yahya Jammeh daga kan mulki.
Ya kara da cewa, suna son su ga canji a kasar a cikin kankanin lokaci da kuma tsari na kusa da na nesa don kawo ci gaba.
Mataimakiyar shugaban kasar Gambiya Fatumata Jallow ta bayyana cewa, gwamnatinsu na aiki don cika alkawarurrukan da Jammeh ya yi wa jama’a.


@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb

'Yan kasar Gambiya sun fara kosa wa da gwamnatin Barrow mai kwanaki 100 ya fara bayyana ne a TRT

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN