• Labaran yau

  Sankarau: Yawan wadanda suka mutu ya kai 438

  A wani rahoto da ya fitar John Oladejo Jami’in cibiyar da ke hana yaduwar cututtuka ta kasa yace kawo yanzu Alkaluman mutane da annobar Sankarau ta kashe a kasar sun kai 438.Yace mamatan sun fi yawa ne a jihar Zamfara.

  A ranar 5 ga watan Afrilu wannan shekarar, mutane 3959 aka tabbatar suna dauke da cutar sankarau, yayin da 181 aka kebe su.Yanzu dai ciwon ya yadu har zuwa jihohi 19 da akasari ke Arewacin kasar, yayin da gwamnati ke cewa an kaddamar da rigakafi.

  Duk da yake rahotanni sun nuna cewa cutar sankarau ta bana daban take ta cutar ta shekarun baya,amma jama'a na dafifi ko cincirindo a wajajen da ake bada allurar rigakafin cutar a jihar Zamfara.

  @isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb

  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Sankarau: Yawan wadanda suka mutu ya kai 438 Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama