Mai Martaba Sarkin Zuru ya fara rangadi a Masarautar saMai Martaba Sarkin Zuru Maj. Gen. (Dr.) Muhammadu Sani Sami CON, Mni, LLD, FICEN, Sami Gomo II ya fara rangadin Kasarsa. Sarkin ya fara ne da Kasar Wasagu a inda yaziyarci Iyayen Kasa biyar dake wannan Masarauta wato Bena, Wasagu, Kanya, Waje da Ribah.
 
A kowace Fada Mai Martaba Sarkin yakan yabawa Gwamnatin Jihar Kebbi a karkashin Senata Atiku Bagudu da kuma ta Tarayya akan irin ayyukan da sukewa Kasa. Sannan yakarbi koken su tareda kira garesu dasu tabbatarda sun sanya ‘ya’yansu Makaranta musamman Mata, ya kara yin kira garesu dasu dawoda tsarin tsaro irin nada inda kowane Basarake ko Mai unguwa zai tabbatar da bakin da ake samu a Kasarsa na kirki ne ko akasin haka tareda kai rahoton batagari a wurin hukuma. 

Koken da Sarakunan wadannan wuraren sukagabatar sun hada da:1. Kira a tallafa wa ilimin mata a Bena ta hanyar gina Makarantar Sakandare ta jeka ka dawo ta Mata a Bena.

2.  Daukar matakin magance matsalolin iyaka tsakanin Bena da Jihar Niger da kuma Ribah da Kasar Dabai.

3.  Gina Banki a garin Ribah.

4.  Gina Dam tsakanin Ribah da Waje.

5. Kara maida Burtullai da mashekarai da kuma mashaya a hannun Fulani don kaucewa fadan Fulani da Manoma.

6.  Kara inganta tsaro a wannan yanki.

7.  Samarwa matasa ayukan yi a Gwamnatin Tarayya.

A jawabinsa na godiya Mai Martaba Sarkin Wasagu Alh. Mukhtar Musa Muhammad Wasagu ya godewa Mai Martaba akan irin kula da yakewa jama’arsa tare da tabbatar masa wannan yanki nasa an samu tsaro da zaman lafiya. Sai abin da ba’arasa ba sannan ya kara gode masa akan irin ayukkan da ake aiwatarwa a wannan yanki.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN