• Labaran yau

  Buhari- Zan cika alkawurra da nayi wa 'yan Najeriya

  Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake jaddada kudiransa na farfado da tattalin arzikin Najeriya musamman alkawurran da ya dauka a lokacin yakin neman zabe.

  A cewar sa gwamnatin sa ta yi nasara a wasu bangarori musammam wajen jaki da cin hanci da rashawa, inda ya ce har yanzu ana kokari wajen gano wadanda suka yi wakaci watashi da dukiyar kasa.

  Shugaba Buhari, ya ce ganin yadda gwamnatin sa ta gaji dimbin bashi daga gwamnatin da ta shude, kuma bai gaji komai a asusun gwamnati ba, ya sa mutane za su rika ganin tafiyar hawainiya a gwamnatin sa, sai dai ya bada tabbacin cewa shirin zai taima wajen farfado da tattalin arzikin Nijeriya.

  @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Buhari- Zan cika alkawurra da nayi wa 'yan Najeriya Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama