Yan fashi sun kashe jami'an 'yan sanda 2 a Sokoto

Ba hoton lamarin bane


Kwamishinan 'yan sanda na jihar Sokoto Mr.Muhammed Abdulkadir ya tabbatar da kashe wasu jami'an 'yan sandan kwantar da tarzoma (Mopol) su biyu da ke aikin gadi a gidan mai na NNPC da ke kan titin Gusau a Birnin Sokoto.


Kamfanin dillancin labarai ta Najeriya NAN ta kara da cewa Kwamishinan 'yan sandan na jihar Sokoto ya kara da cewa 'yan fashin sun yi dakon cinikin gidan mai din ne na ranar Juma'a, Asabar da Lahadi,domin sun kai hari kan wajen ajiyar kudi na gidan mai din bayan sun buda wa jami'an 'yansandan wuta kuma suka kashe su.Rahotanni sun nuna cewa 'yan fashin sun zo da yawa a cikin mota inda suka rijayi jami'an 'yan sandan.

@isyakuweb -Ku biyo mu a Facebook
https://web.facebook.com/isyakuweb

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN