kebbi - Addu'a don Buhari,Gwamnati ta bada Miliyan biyu,ba a ba Malamai ko kwabo ba

Gwamna Atiku Bagudu

A kwanakin baya ne shafin nan na sada zumanta ta Facebook da ake kira”Kebbi Daily Update” ta wallafa wani labari inda ta yi bayani akan cewa jimlar kudi naira miliyan biyu sun salwanta wanda aka ba wa’yanda suka shirya taron Addu’ar kuma aka bukaci a ba Malamai da sauran wa’yan da abin ya shafa kaso daga ciki,a zaman tallafi  da Sadaka ga Malamai da aka gaiyato domin wasu an gaiyato su ne daga wasu kananan hukumomi domin gudanar da Addu’a da aka yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari a babban Masallacin Idi na garin Birnin kebbi ranar Juma’a 24/2/2017 da ta gabata .

A bisa wannan labarin isyaku.com ta kaddamar da bincike akan wannan zargi wanda tuni ya haifar da jite-jite da babu ma’ana balle kyau ga lissafin saurare.Binciken dai ya nuna cewa,bayan da aka kammala wannan Addu’ar ne,aka bukaci wadanda suka shirya wannan taron su je gidan Gwamnati inda mai girma Gwamnan jihar Kebbi ya yi umarni akan cewa aba su Naira Miliyan biyu.Amma da yake lokacin Juma’a ya gabato domin ranar Juma’a ne,sai aka fara bayar da Naira Miliyan daya wanda ake zargin sun fado a hannun wani Malam Adamu,kuma aka raba kudin a tsakanin dukkannin wadanda suke da hannu a wajen shirya wannan taron na Addu'a nan take.

A bisa wannan tsarin ne majiyar tamu ta gano cewa,an sami matsin lamba daga sauran mutane da ke cikin wadanda suka shirya wannan taron ne akan cewa ala tilas sai dai a raba wannan Miliyan daya da aka bayar,saboda su ne suka fara shigowa hannu.A bisa wannan fahimta tsakanin bangaren Malam Adamu da bangaren wani Muhammed Bello Abubakar sai aka raba kudin tare da manufar cewa idan an bayar da cikon Miliyan daya sai a fitar da kaso na Sadaka don Malamai da wadanda abin ya shafa.

Majiyar tamu ta kara da cewa,Muhammed Bello Abubakar ya karbo cikon sauran kudin ,watau miliyan daya daga bisani,amma bai zo ba balle a ci gaba da lissafin da aka faro tun farko a bisa fahimta balle a ware wa Malamai kason nasu da sauran wadanda abin ya shafa.Bayanai sun nuna cewa sauran cikon miliyan daya yana wajen Muhammed Bello Abubakar.A ci gaba da tantance gaskiyar lamarin,isyaku.com ta lalabo lambar wayar salula ta Muhammed Bello Abubakar domin ta samu korafin sa game da lamarin amma wayar salular sa a kashe take tun yammaci jiya har yanzu da aka rubuta wannan rahotun.

Alaramma Ibrahim Bayawa
A yayin da isyaku.com ta tuntubi shugaban hadaddar kungiyar Malami da Limamai ta jihar kebbi Alaramma Ibrahim Bayawa,ya yi bayani akan cewa su kam basu san da zancen ba, amma suna jin rade-raden cewa za'a ba Malamai Miliyan daya na Sadaka,amma  har ya zuwa yau 1/3/2017 basu gan ko kwabo ba.Ya kuma roki Malamai da aka gaiyato su suka baro abin da suke yi,kuma suka zo suka gudanar da wannan Addu’ar don Allah da cewa su yi hakuri,ya kuma kara da cewa ai dama ba domin a ba su wani abu ne suka yi Addu’ar ba illa don Allah. 

Binciken namu ya nuna cewa an gaiyato akalla Malamai 15 wasu ma daga kananan hukumomi ne wanda ya hade rinjayen kungiyoyin Addinin Musulunci da ke cikin jihar Kebbi,amma kuma sai ga wannan lamari ramas dadin ji ya faru.…to me ke faruwa ne a jihar mu ta Kebbi?.Ku karanta labaran da isyaku.com ta bayar akan Addu’ar ranar 23/2/2017 da na ranar Juma’a 24/2/2017.
Isyaku Garba – Birnin kebbi @isyakuweb Ku biyo mu a Facebook

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN