Fassarar wasikar El-rufa'i zuwa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari


Fassarar wasika mai dauke da shafi 30 da Gwamna Malam Nasiru El-Rufai ya aika wa shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari  ranar 22 ga watan Satumba, 2016.
Ga kadan daga cikin wasikar mai dauke da shafuka 30 daga wasu masu kishin kasa.
Wasu Muhimman Shawarwari Ga Mai Girma Shugaban Kasar Nijeriya Muhammadu Buhari – 22 ga watan Satumba, 2016.

Shimfida.

Mai girma shugaban kasa, a watan Afirilu, shekara ta 2015 bayan zaman ka shugaban kasa na rubuto maka wata yar gajeruwar wasika ta shawarwari amma ba mu samu lokaci mun tattauna abin da ta wasikar ta kunsa ba, don ban ma yi tsammani ka samu lokacin dubawa ba saboda irin hidindimun da ke gabanka na shugabanci. Zan so mai girma shugaban kasa ya samu lokaci ya karanta ta tare da wannan ta biyun don ganin irin shawarwari masu muhimmanci da ta kunsa ba tare da wata boyayyen manufa ba. A bisa muhimmancin abin da wancan wasikar ta kunsa ne na sake rubuto maka wannan saboda soyayya ta da ke tsakanina da kai da kuma kishin kasa ya sa na rubuto maka wannan wasika cikin ladabi da biyayya.

Mai Girma Shugaban Kasa, na rubuto maka wannan wasika ce da dayan ma da ta gabata a bisa wasu muhimman b guda uku. Da farko dai burina a siyasance in zama kamar ka. Kuma baicin kai, ba zan taba zama abin da na zama ba duk kuwa da irin suka da caccaka da aka yi ta yi a kaina. Har gobe kuma ina godiya da irin wannan alfarmar da na samu a wurinka. Ranka ya dade, duk wasu ma’aunai ko alkaluma sun nuna kafin zabe da bayan zabe cewa duk wata nasara da na samu ta jingina ne da taka nasarar. In ka yi nasara a mulkinka, ni zan amfana, sannan kuma in ba ka yi nasara ba duk kuwa abin da zan yi a Jihar Kaduna, aikin banza ne saboda zamanka madogara abin jingina gare ni.

A karshe, mai girma shugaban kasa ina mai tabbatar maka cewa kai kadai ka rage mana da za ka iya ceto kasar nan zuwa tudun mun tsira da kuma da dawo wa Arewa da martabarta a riga ganin ta a matsayin wani yanki da ke bayar da gudummuwa wurin cigaban kasa ba wasu ci-ma-zaune ba.
Maigirma Shugaban Kasa, a fili yake don mun karanci siyasarka, mun ga cewa muddan kana raye ba wani dan siyasa da zai yi tasiri a Arewa ya zama shugaban kasa.  Duk wadannan da suke barnatar da dukiyoyinsu da lokacinsu da wasu abubuwa nasu don zama shugaban kasa, ba su fahimci kai zabin Allah ba ne ko kuma Allah dai ya yi su ne don wasu su azurta a karkashinsu ta hanyar yin takara.

Ranka ya dade, kamar yadda na fada maka bayan cin zabenka dole ka sake tsayawa takara a 2019 don cika burinka na farfadowa da dawo da martaba da farfado da tattalin arziki da kawo adalci mai dorewa a Nijeriya. Don haka muna bukatar nasarar ka don ita ce tamu nasarar musamman mu da muke biye da kai a siyasance.

Maigirma Shugaban Kasa, kamar yadda na rubuta a wasikata ta farko a watan Afrilu 2015 cewa ka gaji manya manyan matsaloli ta fuskar siyasa da tattalin arziki da kuma shugabanci wadanda ba hannunka cikin ‘kirkiransu amma yanzu dole ka magance su. Wadannan matsaloli da ka gada sun kara ninninkuwa saboda faduwar farashin man fetir da kuma ta’addancin Tsagerun Naija Delta da ya mayar da man da ake haka ya ragu da kashi 50.

Har cikin zuciyata, ina ganin kamar  Jami’iyyarmu ta APC ta  gaza ganin yadda mutane ke son duk yadda za mu , mu yi kawai don ganin mun saita kasar nan komai ya zama daidai kamar yankan wuka cikin kankanin lokaci musamman ta fuskar shugabanci. In ban da nasarar da muka samu ta yaki da Boko Haram da cin-hanci da rashawa, ranka ya dade, har cikin masu goyon bayanmu wasu na ganin mun gaza. Saboda wadannan dalilai ne ya sa na rubuta wannan takarda don ba ka shawarwari a wasu bangarori muhimmai guda uku da suka hada da bangaren siyasa da tattalin arziki da kuma fannin shugabanci.

2. Fannin Siyasa:

Maigirma Shugaban Kasa, na san ba ka manta da irin matsanancin halin da muka shiga a jam’iyyarmu tun wurin rijista da fitar da dan- takara da kuma wurin tarukkanmu na shugabannin jam’iyya, da kuma irin muguwar rawar da wasu kungiyoyi suka taka a cikin jam’iyyar. Na san nasarar da muka samu ba ta rasa nasaba da goyon bayan da shugabannnin jam’iyyar suka bayar amma ba wai don sun ilahirin ‘yan jam’iyyar ba.

Haka dai ya ci gaba da ba Maigirma shigaban kasa shawara har a karshe ya kammala da :
Abin dai jin dadi, shi ne rahamar Allah na tare da mu tun daga ranar da Allah ya kawo jam’iyyarmu ta APC, sannan miliyoyin zakakuran matasa na nan tare da kai kuma a shirye suke don ganin ka samu nasara a shugabancin kasar nan.

Da fatan wannan wasikata, za ta samu wata tasiri ta kasancewa cikin jerin shawarwari da ake ba ka don ganin ka samu nasara wurin shugabancin kasar nan. Ina maka fatan Allah ya dafa maka wurin sauke nauyin da Allah ya daura maka wurin  kawo cigaba  da dawo da zaman lafiya mai dorewa a kasar baki daya.
Kuma ina da tabbacin cewa kana sane a  shirye nake ko da yaushe don yin duk abin da zai kawo samun nasara a mulkinka.

Naka mai biyayya

Nasir Ahmed El-Rufai

Labarai24

@isyakuweb  Ku biyo mu a Facebook
https://web.facebook.com/isyakuweb

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN