• Labaran yau

  ABU Ta Mayarda Martani Game Da Zargin Da Ake Yi Wa Dino Malaye

  Jami’ar Ahmadu Bello Zaria ABU ta ce ba za ta fitar da wasu bayanai ba game da zargin da ake yi wa sanata Dino Malaye na amfani da takardun jabu saboda bai kammala karatun sa ba a jami’ar.
  Wannan na zuwa ne bayan da jami’ar ta ki fitar da bayanai akan batun a ranar Larabar da ta gabata, kamar yadda ta yi alkawari.
  Daraktan yada labarai na jami’ar, Adamu Mohammed, ya fadawa manema labarai a jiya Alhamis cewa hukumomin jami’ar sun tattauna akan batun, sai  dai bai bayyana ko me suka tattauna ba.
  Sai dai ya ce sun yanke hukuncin ba za su fitar da bayanai akan al’amarin ba saboda binciken da majalisa take yi akai.
  Haka kuma ya ce duk wanda yake bukatar tantance gaakiya takarsun wani tsohon dalibin makarantar, toh ya bi hanyoyin da jami’ar ta shinfida.
  A makon da ya gabata ne Jaridar Sahara Reporters ta wallafa wani rahoto da ke zargin sanata Dino Malaye da amfani da takardun makaranta na jabu.
  Sai dai sanatan ya karyata wannan batu. A fadarsa, “ba zai yiwu ace ban kammala karatuna ba a ABU, sannan na iya yin degree na biyu. Yanzu haka na 3 nake yi”.


  (Mujallarmu)
  @isyakuweb--Ku biyo mu a Facebook
   
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: ABU Ta Mayarda Martani Game Da Zargin Da Ake Yi Wa Dino Malaye Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama