An kashe matashi a garin Jega,an jefar da gawar a gefen titin Jega-Sokoto

Wani labari da jaridar Dailytrust ta wallafa ranar Lahadi 19/2/2017 dangane da kisan wani matashi mai suna Zayyanu Garba wanda ake zargin wasu mutane da aikatawa bayan sun yi shigar sojan gona suka tafi da shi marigayi Zayyanu da abokin sa Mudassir dukkan su 'yan shakara 27 zuwa wani gida a cikin garin Jega,babban garin karamar hukumar mulki ta Jega a cikin Jihar Kebbi,inda suka azabtar da matasan guda biyu,al'amarin da yayi sanadin mutuwar shi Zayyanu.

Jaridar ta kara da cewa,mutanen sun ce wai su jami'an tsaro ne kafin su tafi da marigayin da abokin sa zuwa inda suka azabtar da su.Bayanai sun nuna cewa bayan kisan shi mamacin an dauki gawar shi inda aka jefar da ita a gefen titin Jega zuwa Sokoto wanda ake tsammanin da dare ne aka yi wannan danyen aikin.Jaridar ta kara bayar da haske akan irin bayanai da hujjojin da wanda abin ya shafa ya bayar wanda tare da shi ne mutanen suka kama shi da marigayi Zayyanu,wanda shi ma akwai ranukkan duka a jikin sa.

Mahaifin marigayin Malam Abubakar Tafida Jega ya nuna mamaki da al'ajabi a kan yadda har yanzu hukuma bata kama kowa ba dangane da wannan al'amarin,duk da yake ya yi kara a wajen wadanda ke da hakkin sauraren karan,ya ce haryanzu cewa ake masa ana kan bincike,duk da yake yau kwana 10 kenan da faruwar al'amarin.

Jaridar ta kara da cewa ta tuntubi kakakin hukumar 'yan sanda na jihar kebbi ASP Mustapha Suleiman ya tabbatar da cewa an sami gawar Zayyanu ne a hanyar Jega zuwa Sokoto.Rahoton ya nuna cewa mahaifin marigayi Zayyanu na shirin kai koke zuwa hukumar kare 'yancin bil'adama da ke Sokoto domin ta taimaka masa a cikin wannan al'amarin mai rudani.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN