• Labaran yau

  AN TSINCI JARIRI A WANI KANGO A GARIN AMBURSA A JIHAR KEBBI

  An Tsinci Jariri A Wani Kango A Garin Ambursa Ta Jihar Kebbi
  Hukumar Hisba ta jihar Kebbi na bada sanarwar an kawo mata wani yaro jariri sabon haihuwa wanda aka ajiye a cikin wani kangon gida a garin Ambursa dake karamar hukumar mulki ta Birnin Kebbi.
  An tsinci jaririn ne cikin buhu, yana kuka, a ranar Juma'ar da ta gabata da misalin karfe 2:30 yamma.
  Hukumar na kira ga jama'ar yankin na Ambursa da duk wanda ya san uwar wannan yaro ko kuma wata da ake tuhuma da nata ne da a sanar da hukuma don daukar matakin da ya dace.
  Sanarwar na dauke da sa hannun mataimakin shugaban Hisba na jihar Kebbi, Alhaji Mamuda Geza
  RARIYA
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: AN TSINCI JARIRI A WANI KANGO A GARIN AMBURSA A JIHAR KEBBI Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama