GWAMNA DA DAN MAJALISA SUN YI DAMBE Wasu gagga-gaggan shahararrun yan siya, kuma shuwagabannin al’ummar sun dambace yayin gudanar da yakin neman zabe, inda suka dinga kai ma juna naushi, tokari da hantara.
Wannan lamari ya faru ne a kasar Kenya yayin da jam’iyyar ‘Orange Democratic Movement Party’ (ODMP) taje yakin neman zabe a wanni yankin kasar, inda Gwamna Cyprian Awiti da dan majalisa Oyugi Magwanga, wakilin jama’a Kasipu-Kabondo suka dambace sakamakon cacar baki data shiga tsakaninsu.
Wannan abin kunya ya faru ne a gaban dubun dubatar mutane, da kyar tsohon shugaban kasa Raila Odinga ya samu daman raba su.Damben nasu ya kai dambe tunda har sai da suka kai juna kasa. Rikicin dai ya samu asali ne lokacin da wasu magoya bayan gwamna Awiti ke kirar ya kamata a kara zaben gwamnan a zabukan 2017, amma kuma a dawo da Magwanga saboda a cewar su bai tabuka komai ba a majalisa.

Daga Muhammad Auwal naij.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN