Yan Najeriya ka iya yi wa gwamnatin shugaban kasa Buhari bore inji matar sa Aisha Buhari

Aisha Buhari
Daga BBCHausa
'Yan Nigeria ka iya yi wa gwamnatin Buhari bore — Aisha Buhari Sa'o'i 2 da suka wuce Aika Hirar BBC da Aisha Buhari na tayar da kura Uwargidan Shugaban Najeriya, Aisha Buhari, ta ce tana ji wa mijinta tsoron kada mutanen da suka zabe shi su yi masa bore. A wata hira da ta musamman da BBC, ta ce gwamnatin mai gidanta ya yi watsi da fiye da rabin mutanen da suka yi mata wahala har ta samu mulki. Ta ce shugaban bai mafi yawan mutanen da ya nada a cikin gwamnatinsa ba. Ta kara da cewa wasu "'yan tsiraru" ne suke juya akalar gwamnati, inda suke zabar mutanen da ake bai wa mukami. Bayanin da Mista Buhari ya yi a lokacin da aka rantsar da shi cewa, "babu wanda zai juya shi, kuma shi na kowa ne," ya ja hankalin mutane sosai. Sai dai kalaman na matarsa, da ma wadanda wasu masu kusanci da gwamnatin ke fada, na nuni da cewa lamarin ba haka yake ba. A cewarta, "Shugaban bai san mutane 45 daga cikin 50 (alal misali) da ya nada ba, kuma ni ma ban sansu ba duk da cewa na shafe shekaru 27 tare da shi". Aisha Buhari ta roki wadanda ta ce suna hana ruwa gudu da su tausayawa jama'a su daina abin da suke yi, sai dai ba ta kama sunan kowa ba. Ta kara da cewa ba ta jin dadin yadda ake tafiyar da mulkin kasar. Image copyrightGETTY IMAGES Image caption Mutane da dama na zargin gwamnatin Shugaba Buhari da rashin sanin alkibla A cewarta, "Mutane da yawa sun fara rarraba kawunan 'yan jam'iyyar APC, kuma hakan yana kawo mana damuwa da yawa yanzu. Saboda suna ganin su suka yi wahala amma ba sa koina yau". Ta kara da cewa, "Wadanda ba su yi wahala ba; ba su da katin zabe su suka zauna a kan mutane suke yin komai da komai. Abin da nake guje musu (su manyan APC) shi ne boren da mutum miliyan 15 za su yi". An tambayi Misis Buhari ko mai gidanta ya san da wannan korafi, sai ta ce "ko ya sani ko bai sani ba wadanda suka zabe shi sun sani. Babu kuma abin da zan gaya masa don yana kallon abin da ke faruwa". Ko wanne hukunci ta yanke? Uwargidan shugaban na Najeriya ta ce Shugaba Buhari bai san akasarin mutanen da ya nada a mulki ba, tana mai cewa yawancin mutanen da ke tare da shi 'yan-ta-yi-dadi ne. "Cikin wadanda ya zaba ya nada idan an tambaye shi 45 cikin 50 ba saninsu ya yi ba. Bai san su ba. Haka nake zato. Ni ma ban san su ba saboda na zauna da shi shekara 27," a cewar ta. Wannan wani bangare ne na hirar da muka yi da ita, inda a ranar Litinin ta yi magana kan irin aikace-aikacen da ofishinta ke gudanarwa domin tallafawa mata masu karafin karfi da kuma 'yan gudun hijira a Arewa maso Gabas. Aisha Buhari ta ce mai gidan na ta bai gaya mata matsayinsa kan sake tsayawa takara a shekarar 2019, tana mai cewa "amma ni na yanke hukunci". Sai ku kasance tare da mu a shirinmu na Gane Mini Hanya na ranar Asabar domin jin hukuncin da ta yanke da ma cikakkiyar hirarmu da ita. 'Yan Nigeria ka iya yi wa Buhari bore — Aisha Buhari Wasu daga cikin tambayoyin da Naziru Mikailu ya yiwa Aisha Buhari: Zargin karkatar da kayan tallafi ga 'yan gudun hijira a Borno Su wane ne mutanen da suka kewaye Shugaba Buhari? Anya Shugaba Buhari ne ke jan ragamar gwamnatin kuwa? Kin yarda da abin da mutane ke cewa wasu 'yan tsirarun mutane ne ke tafiyar da gwamnati? Ko ya gaya mata cewa zai tsaya takara a zaben 2019 Idan zai tsaya za ta goyi bayansa? Su wanene wadanda aka yi watsi da su a APC? Ya za ki kwatanta rayuwarku kafin ku hau mulki da kuma yanzu? Kamar sa'o'i nawa kike iya samu a rana tare da mai gidanki? Shin kin shaida masa cewa akwai matsala a tafiyar nan? Me za ta ce game korafin da ake yi cewa tana yawan tafiye-tafiye? A ina take samun kudaden da take gudanar da ayyukan ofis dinta? Kada ku manta za ku iya kallo da sauraren hirar a talabijin da shafunmu na intanet, bbchausa.com

1 Comments

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

  1. Lallai akwai matsala a gidan Buhari balle Najeriya,idan dai har matar sa ce ke wannan zancen da kan ta,to wallahi dole ne Buhari ya gyara tsarin sa kafin abin da ba a so ya faru na tarzoman talakka.

    ReplyDelete
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN