An kori 'yar wasan kwaikwayon Kannywood Rahma Sadau

Rahma Sadau


Kungiyar da ke sa ido ka tarbiyya da ka'idodin yadda ake gudanar da harkar hotuna masu motsi watau  motion pictures a arewacin Najeriya watau MOPPAN,ta kori jaruma Rahma Sadau daga shiga ko sake bayyana a cikin kowane irin shiri matsawar bidiyo ne na wasan kwaikwayo ko nishadantarwa a aewacin Najeriya.Wannan hukuncin ya samo asali ne bayan Rahma  ta baiyana a wani  faifan cd ta wakar CLASSIQ wanda ke zaune a garin Jos na jihar Plateu.Ita dai kumgiyar MOPPAN cewa tayi ta dauki wannan matakin ne sabota an nuna rashin dattaku ta hanyar rungume rungume da aka yi tsakanin ita Rahama da shi ClassiQ a cikin wannan video wanda ya saba wa ka'idan addini da zamantakewa al'adar kasar hausa na arewacin Najeriya.
A jawabin da ta fitar a wasu kafofin sada zumunta na yanan gizo,Rahama ta ce ita bata yi wani abin da ya saba ka'ida ba domin waka da akayi waka ce ta soyayya,wanda ita a matsayin ta na jarumar wasan kwaikwayo,ta bi umarnin abin da aka ce ta yi ne,ta ce amma idan hakan ya saba,ko ya bata ma mutane rai,to ta nemi afuwa kuma ta dau alhakin duk abin da ya same ta.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN