GAME DA MU

Na buda wannan shafin ne domin samar da labarai musamman na Jihar Kebbi sakamakon rashin
wadatar Mawallafa da Marubuta masu zaman kansu wadanda suka sa dukiya da kuma lokacinsu domin samar da labarai na jihar Kebbi ta hanyar yanar gizo.Sa'ilin da labarai na gida jihar Kebbi basu samu ba sai mu samo labarai na Nishadantarwa kamar labaran al'ajabi wadanda su ne muka fi bayar da karfi akansu domin bincike da muka yi ya nuna cewa irin wadannan labaran jama'a suka fi karantawa.

Ni Isyaku Garba asali 'dan kudancin jihar Kebbi ne daga Masarautar Zuru, tsohon jami'in hukumar tsaro na DSS, Marubuci, Masani harkar ingizon wayar salula da sadarwar zamani, Manazarci akan harkar tsaro kuma 'dan jaridar zamani kuma Mawallafi.Na yi karatun harkar Jarida ta yanar gizo daga cibiyoyi da dama daga ciki har da Makarantar koyon aikin jarida na BBC.

ISYAKU.COM yana da ma'aikata da ke aiki karkashinsa guda uku da wakilai hudu a fadin jihar Kebbi kawo yanzu.

Muna maraba da ku a ko da yaushe.GAME DA MU GAME DA MU Reviewed by on February 11, 2018 Rating: 5

ISYAKU TV

Ku dakace mu
Powered by Blogger.