Za mu roki shugaba Buhari ya tsaya takara a 2019 - Abubakar Malami

Ministan shari'a na Najeriya Abubakar Malami ya ce za su roki shugaba Muhammadu Buhari domin ya saka tsayawa takara a 2019.

Ministan ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya kai ziyara a ofishin BBC a London kwanakin baya.

BBC ta ruwaito cewa Ministan ya ce "Mu a shirye muke mu roke shi da ya sake tsayawa takarar saboda ganin abubuwa na alkairi da shugaban ya faro a kasar sun wanzu."

Yayin da aka tambayi ministan ko zai amsa kiran nasu, ganin cewa su mukarrabansa ne.
Sai ya kada baki ya ce "za mu tsananta roko."


Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
Za mu roki shugaba Buhari ya tsaya takara a 2019 - Abubakar Malami Za mu roki shugaba Buhari ya tsaya takara a 2019 - Abubakar Malami Reviewed by on December 17, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.