Soji sun bindige wani kwamanda mai hada wa boko haram boma-bomai

Rundunar soji ta Brigade na 21 tare da hadin guiwar runduna ta 121 da ke fada da Boko haram a yankin Borno sun yi nassarar bindige wani babban kwamanda a  boko haram wanda fitacce ne wajen hada boma-bomin a cikin kungiyar ta boko haram.
 
Sakamakon wani bayanan sirri da rundunar ta samu, sai rundunar ta bi diddigin lamarin har zuwa inda suka yi masa kwanton bauna suka kashe shi a yayin da yake kokarin ketarawa a yankin Firgi a karamar hukumar bama.

A kashe biyu daga cikin 'yan boko haram yayin da sauran suka ranta na kare da raunukan al'barushi

Rundunar sojin ta kama bindiga kirar AK47 guda daya, da fankon Magazine,  babura biyu da takardar shedan zama 'dan kasa.Haka zalika sojin sun mai da wa masu shanaye shanayensu da aka sace.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
Soji sun bindige wani kwamanda mai hada wa boko haram boma-bomai Soji sun bindige wani kwamanda mai hada wa boko haram boma-bomai Reviewed by on December 26, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.