Rikicin Manoma da Makiyaya a yankin Aljannare/Bagudo,Yombe ya bukaci a zauna lafiya

An yi kira ga Makiyaya da ke yankin Aljannare da Bagudo cewa su zauna lafiya tare da bin doka da oda,wannan jawabin ya fito ne daga bakin wakilin Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu watau Mataimakin Gwamna  Alh. Samaila Yombe Dabai yayin da ya kai ziyarar gaggawa a fadar Uban kasa na Aljannare da yammacin Litinin.

Bayanai sun nuna cewa an sami wata hatsaniya sakamakon karewar wa'adi da Kotu ta bayar akan karar da shugabannin Fulani suka shigar akan jayayyar da ake yi tsakanin Manoma da Makiyaya akan wani yanki da ke bakin iyaka tsakanin Aljannare da Bagudo inda Makiyaya suke amfani da wurin domin kiwon dabbobin su.

Kotu ta tabbatar wa al'ummar Fulani da gurin a wani hukunci da ta yanke kamar yadda Uban kasar Aljannare Alh. Abubakar Saddiq Aljannare da DPM na karamar hukumar Suru/Dakingari Alh. Yahaya Lailaba suka shaida wa Mataimakin Gwamna.Haka zalika sun ce Kotu ta ba da zuwa 19/12/2017 domin Manoma su kawashe nasu-ya-nasu su bar gurin.

Wani bayani da muka samu ya nuna cewa cikar wa'adin ke da wuya sai wasu suka bukaci ala tilas Manoman su fice daga yankin sakamakon haka ya sa rigimar ya barke.

Mataimakin Gwamna Alh. Samaila Yombe ya bukaci shugabannin al'umman Fulani da suka halara a fadar Uban kasar Aljannare akan cewa su yi hakuri su zauna lafiya kuma su bi doka da oda, yayin da shi Mataimakin Gwamna zai gabatar da matsalar ga Maigirma Gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Bagudu domin samun mafita. Amma kafin haka, Yombe ya bukaci shugaban Karamar hukumar Suru akan cewa ya rubuta takarda na sanar da wadanda abin ya shafa dangane da umarnin na Kotu.

Yombe ya kara da cewa duk da yake an ci ma wa'adin ranar 19 ga watan Disamba da Kotu ta bayar akan lamarin , yana da kyau a yi ma Manoman uzuri domin su girbe amfanin gonarsu da sauran ababe da ya kamata a dauka kafin a aiwatar da umarnin na Kotu domin a kauce ma barkewar fitina.

Ziyarar ya samu halarcin Kwamandan rundunar tsaro ta NSCDC na jihar Kebbi ,wakilin Kwamishinan yansanda na jihar Kebbi watau DPO na Suru da wakilin Darakta DSS na jihar Kebbi.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
Rikicin Manoma da Makiyaya a yankin Aljannare/Bagudo,Yombe ya bukaci a zauna lafiya Rikicin Manoma da Makiyaya a yankin Aljannare/Bagudo,Yombe ya bukaci a zauna lafiya Reviewed by on December 20, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.