Shahararren dan wasan kwaikwayon Hausa Kasimu Yaro ya rasu

Shahararren dan wasan kwaikwayon nan na wasan Hausa Kasimu Yaro ya rasu ranar Assabar 3,Satumba 2017 a gidansa da ke rukunin gidaje na Marafa Estate a Kaduna.

Marigayi Kasimu Yaro ya rasu yana da shekara 70 kuma an yi jana'izansa bayan Sallar La'asar ranar Lahadi a Masallacin Maiduguri Road a Kaduna.

Za'a tuna Kasimu Yaro a rawa da ya taka a finafinan Hausa da kuma wasan kwaikwayo na gidan talabijin na NTA  musamman shirin "Magana jarice".


Shafin mu na Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Shahararren dan wasan kwaikwayon Hausa Kasimu Yaro ya rasu Shahararren dan wasan kwaikwayon Hausa Kasimu Yaro ya rasu Reviewed by on September 03, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.