• Labaran yau

  July 13, 2017

  'Yan sanda sun bindige wasu 'yan fashi da ke addaban hanyar Zaria-Kano

  Dubun wasu  'yan fashi ya cika sakamakon bindigesu har lahira da 'yansanda sukayi a kusa da kauyen Garun Malam a kan titin Zaria zuwa Kano a ranar 10 ga watannan da misalin karfe 9 na dare bayan sun tare haya suna fashi.

  'Yan fashin sun gamu da rashin sa'a ne sakamakon zuwar motar 'yansanda da take  wucewa sai yan fashin suka buda masu wuta ta hanyar harbi da bindigogi su kuma 'yansanda suka maida martani da harbin da ya sha karfin bindigogin 'yan fashin.

  Nan take aka bindige biyu daga cikin 'yan fashin yayin da saura suka ranta na kare zuwa cikin daji wasu daga cikinsu suna dauke da raunukan albarushi.

  'Yansanda sun sami bindiga kirar AK47 guda daya da albarushi 12,tocila da wasu layu na sammu.

  Mai magana da yawun hukumar 'yansanda na jihar Kano DSP. Magaji Musa Majia ya bukaci a kai rahotu ga hukumomi idan aka gan wani ko wasu da raunukan albarushi.

  Ku biyo mu a shafin mu na Facebook @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari. Kana da sha'awar taimaka mana da Labarai, ko sharhi ? ka kira mu a 08062543120. Shiga shafinmu kai tsaye domin samun cikakkun Labarai.Ka shiga www.isyaku.com a browser ko opera ko firefox ko safari na wayarka zaka sami cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: 'Yan sanda sun bindige wasu 'yan fashi da ke addaban hanyar Zaria-Kano Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama