• Labaran yau

  July 18, 2017

  Wani shugaba a jam'iyar APC ya sha dukan tsiya a jihar Delta

  Yayin da fagen siyasar Najeriya ke ci gaba da kasancewa fagen dambaruwar ababen kunya da rashin ragowa ga su  kansu 'yan siyasa,wani shugaban jam'iyar APC a karamar hukumar Uvwie a jihar Delta ya sha dukan tsiya a hannun 'yan bangan siyasa wanda bayan sun likida masa duka suka kuma tube shi zindir.

  Mr Eddy James Onajite shine shugaban jam'iyar APC a ward na 8 a karamar hukumar.

  Bayanai sun nuna cewa 'yan bangan siyasa da suka tare tawagar Sanata Ovie Omo-Agege kuma suka ci zarafinsa ranar Asabar da ya gabata sune kuma suka aikata wannan danyen aikin wa shugaban na APC a karamar hukumar Uvwie.

  Haka zalika a garin Birnin kebbi,a 'yan makonnin da suka gabata wani matashi mai suna Muhammed Bello ya sha duka a hannun wani dan bangan siyasa da ke tare da wani dan siyasa sakamakon wani tattaki da shi Muhammed Bello ya shirya don nuna adawa da abin da suka kira "yin ba daidai ba " .  Ku biyo mu a shafin mu na Facebook @isyakuweb https://www.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari. Kana da sha'awar taimaka mana da Labarai, ko sharhi ? ka kira mu a 08062543120. Shiga shafinmu kai tsaye domin samun cikakkun Labarai.Ka shiga www.isyaku.com a browser ko opera ko firefox ko safari na wayarka zaka sami cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Wani shugaba a jam'iyar APC ya sha dukan tsiya a jihar Delta Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama