Ku rage hawa Facebook, WhatsApp da Instagram – Sultan

Shugaban majalisar koli ta lamurran addinin Islama a Najeriya, ya gargadi yara musamman 'yan mata da su guji daukar lokaci mai yawa...

Shugaban majalisar koli ta lamurran addinin Islama a Najeriya, ya gargadi yara musamman 'yan mata da su guji daukar lokaci mai yawa kan shafukan sada zumunta na zamani domin yin hakan ka iya bata tarbiyarsu.
Da yake jawabi a wajen wata gasar musabakar Alkur'ani mai girma a birnin Sakkwato ranar Lahadi, Sultan Saad Abubakar, ya ce, "abin damuwa ne matuka" ganin irin yadda shafukan sada zumunta kamar su Facebook da Whatsapp da Instagram da 2go ke dauke wa yara hankali daga karatunsu.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ambato shi yana cewa ya kamata iyaye su rinka kula da yaransu.

''Irin yadda 'yan mata ke bata mafi yawan lokutansu a kan shafukan sada zumunta abin damuwa ne kuma wannan yana da hadari ga al'ummarmu.

Yara mata su ne kashin bayan tarbiyya da kuma ci gaban al'ummarmu don haka idan suka kauce hanya, to dukkanin al'umma za ta shiga hadari domin su ne iyayenmu kuma masu yi wa yaranmu tarbiyya.''

Ya yi kira ga iyaye da su tabbatar da cewa 'ya'yansu mata sun yi amfani da lokacinsu wajen yin abubuwa masu ma'ana da rayuwa, ciki har da karatun Alkur'ani, domin yin hakan ne zai sa su zamo iyaye na-gari".

An dade an nuna damuwa kan illar shafukan sada zumunta ga tarbiyyar yara, musamman mata duk da irin farin jini da shafukan ke da su a tsakanin al'umma musamman matasa.

Ma'abota amfani da shafukan sada zumunta wadanda suke tattauna muhimman al'amura suna yawan korafi cewa, a kan samu 'yara marasa tarbiyya' su dinga zagin mutane kan wata mas'ala da ake tattaunawa a kanta, ba tare da la'akari da cewa mutum ya girme su ba.

"Al'amarin ba dadi sam, sai ka ga kanin bayanka ya zo shafinka ya dura maka zagi don kawai wani ra'ayinka da ka bayyana bai zo daidai da nasa ba," in ji wani mai amfani da shafukan sada zumunta da ya bukaci a boye a sunansa.

Ita ma wata ma'abociyar amfani da shafukan sada zumuntar Safiyya Abbas, cewa ta yi, "Ai gaskiya abin ba dadi musamman yadda 'yan mata ke baje kolin tsiyarsu a Instagram da wallafa hotuna masu nuna tsiraici da sauran su, dole kan iyaye su tashi tsaye."
Ku biyo mu a shafin mu na Facebook @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari. Kana da sha'awar taimaka mana da Labarai, ko sharhi ? ka kira mu a 08062543120. Shiga shafinmu kai tsaye domin samun cikakkun Labarai.Ka shiga www.isyaku.com a browser ko opera ko firefox ko safari na wayarka zaka sami cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.

Daga BBC

COMMENTS

Name

AL-AJABI,25,BIDIYO,1,BIRNIN-KEBBI,25,DUNIYA,23,FADAKARWA,23,FASAHA,3,HOTUNA,39,JAKAR MAGORI,18,LABARI,416,NISHADI,51,SANARWA,13,SHARHI,13,SIYASA,17,TARIHI,7,WASANNI,8,
ltr
item
ISYAKU.COM: Ku rage hawa Facebook, WhatsApp da Instagram – Sultan
Ku rage hawa Facebook, WhatsApp da Instagram – Sultan
https://4.bp.blogspot.com/-K6rlib5NcYg/WWNtngnFBYI/AAAAAAAAFlU/6-FlK5SY4eUQZ2fsz6269tSfBN8JW9F_gCLcBGAs/s320/SULTAN.jpg
https://4.bp.blogspot.com/-K6rlib5NcYg/WWNtngnFBYI/AAAAAAAAFlU/6-FlK5SY4eUQZ2fsz6269tSfBN8JW9F_gCLcBGAs/s72-c/SULTAN.jpg
ISYAKU.COM
http://www.isyaku.com/2017/07/ku-rage-hawa-facebook-whatsapp-da.html
http://www.isyaku.com/
http://www.isyaku.com/
http://www.isyaku.com/2017/07/ku-rage-hawa-facebook-whatsapp-da.html
true
3052478943858316060
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts KARANTA SAURAN LABARAI Karanta saura Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All KARANTA WADANNAN LABEL MAADANI BINCIKA GABADAYAN LABARAI Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS CONTENT IS PREMIUM Please share to unlock Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy