• Labaran yau

  July 25, 2017

  An kori 'yansanda 3 daga aiki akan laifin kwace N50.000

  Hukumar 'yansanda ta kori wasu 'yansanda guda uku a bisa kamasu da laifin kwace,kamawa da tsare wani matashi ba bisa ka'ida ba da gudanar da ayyuka wanda suka sabawa ka'idar aikin dansanda.

  Wadanda aka kora sun hada da  Inspector Okelue Nkemeonye with Administrative Police Number, 136005; Sergeant Braimoh Sunday, with Force Number, 355897, and Yusuf Olukoga with F.No., 359928.
  Dukkannin yansandan suna aiki ne a sashe na N a Ijede,Ikorodu jihar Lagos.

  Rahotanni sun nuna cewa a ranar 21/6/2017 'yansandan sun kwace N50.000 daga wani matashi bayan sun tuhume shi da kasancewa dan yahoo.A nashi bayani  matashin yace "a ranar 21,6 na je banki a unguwar Ikorodu domin in sa kudin yaya na N1 million a banki,amma aka sami matsalar layin yanar gizo(network) saboda haka sai na sa kudin a asusun ajiya na domin daga bisani in tura ma yayan nawa kudinsa saboda haka zaifi sauki."

  "Bayan na fito daga bankin ne kawai sai wadannan 'yansanda suka dora min bindiga a kai suka ce in shiga motarsu wanda nan take na shiga.Daga bisani suka kwace wayar salula na kuma suka tambaye ni ko miye nike yi a rayuwa,na gaya masu cewa na kammala Degree amma bani sa aiki a yanzu.Daga bisani sai shaidar hulda da nayi da banki (alert) ya shigo cewa na sanya N1 million.Daga nan sai suka kama ni da duka bayan sun kaini Ofishinsu na SARS."

  "Daga bisani suka karbi naira N50.000 daga wurina kuma suka karbi N200.000 daga wajen wasu mutane da aka tsaremu tare da su a ofishin."

  Matashin ya rubuta koke zuwa sashen kula da da'a da harkokin cin hanci da rashawa na hukumar 'yansanda ta Whatsapp na hukumar a 08057000003 wanda daga bisani suka bi diddigin lamarin da ya kai ga koran batagarin 'yansandan.  Ku biyo mu a
  https://www.facebook.com/isyakuweb
  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye.
  Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
  Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An kori 'yansanda 3 daga aiki akan laifin kwace N50.000 Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama