'Yan Shi'a sun gudanar da Mauludi sakamakon kammala salati Miliyan 5 ga Manzon Allah | isyaku.com

Kungiyar 'yan uwa  Musulmi da aka fi sani da Shi'a sun gudanar da taron Mauludi sakamakon kammala salatin Manzon Allah guda miliyan 5,Sayyidina Zara miliyan 3,Sayyidina Ali miliyan 3 yayin da Imam Hassan da Hussaini da sauransu suka sami salati  miliyan biyu a kowannensu a cikin sauran Imamai masu daraja da suka rage wanda ya samar da jimilar salati miliyan 33 gaba daya.

Majiyar mu ta shaida mana cewa an buda taron da addu'a a yayin da Mal.Habibu Bello ya fara gabatar da jawabi kan muhimmancin salati ga Manzon Allah da falalar da ke ciki.

Mal.Umar M/gandu yayi nasiha cewa yana da kyau idan aka haifa wa mutum yaro ya sa masa sunan Manzon Allah,ya cigaba da cewa "akwai Hadisi da yace idan aka haifa wa mutum yara uku maza kuma bai sanya wa daya daga cikin su sunan Manzon Allah ba kamar yayi wa Manzon Allah jifa'i ne"

An gabatar da lakca-lakca da nasiha daga Malamai da kuma wakokin zikiri ga Manzon Allah.
@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka aiko mana rahotu ? ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com
'Yan Shi'a sun gudanar da Mauludi sakamakon kammala salati Miliyan 5 ga Manzon Allah | isyaku.com 'Yan Shi'a sun gudanar da Mauludi sakamakon kammala salati Miliyan 5 ga Manzon Allah | isyaku.com Reviewed by Isyaku Garba on June 11, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

Powered by Blogger.