Raddi: Sani Dododo "Ba wanda ya ba Mawaka kudin talakawan jihar Kebbi" | isyaku.com

Mai magana da yawaun jam'iyar APC kuma daya daga cikin manyan jigogi a cikin jam'iyar a jihar Kebbi Alh.Sani Dododo ya kalubalancin masu yada jita-jita da zarge-zargen musamman a shafukan sada zumunta na yanar gizo cewa Gwamnati ta kwashi kudin jiha ta baiwa Mawaka da Makada a bikin ranar Dimokaradiya da aka gudanar a makon da ya gabata.

Alh.Sani ya ci gaba da bayani inda yayi nuni da irin kokarin da Mawaka da Makada suka yi ta yi kuma ba tare da an basu ko sisi ba a lokacin da suke tallata jam'iyar APC kafin jam;iyar ta ci zabe.Ya kara da cewa ba'a biyasu ladan kokarin da sukayi ba idan aka yi la'akari da gudunmawa da suka bayar wajen tallata jam'iyar ta hanyar hazakar su ta waka.

Alh.Sani Dododo yace "Na kalubalanci kowaye yake wannan maganar ya kawo hujja inda aka debi kudin talakawa aka baiwa Mawaka,a duk cin kyautuka da aka bayar mutane ne daidaiku suka dinga bayar da taimako ga wadanda suka nuna hazaka ciki har da injiniya da ya kirkiro injin na ban ruwa da sauransu ".

"Idan har an bayar da taimako wa Mawaka suma ba yan Najeriya bane,ko kuwa suma basu yi zabe ba,?...masu yin wannan zancen suna nuna adawa ne kawai akan irin ci gaba da Gwamanatin APC ta samu a jihar Kebbi da Najeriya cikin shekaru biyu kawai".

Jigon na jam'iyar APC ya bukaci jama'a su sanya tsoron Allah a zukatansu kafin su yi furuci,musamman akan lamuran da basa da shaida ku hujja akai.Ya kuma yi nuni da manyan ayyuka da Gwamnati take yi a jihar Kebbi kamar bangaren kiyon lafiya,noma,ilimi da sauransu,Gwamnati ta zuba miliyoyin kudi akan inganta rayuwar talakan jihar Kebbi ta fannoni da yawa.




@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka aiko mana rahotu ? ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN