• Labaran yau

  June 05, 2017

  Kebbi: Mutum 25.000 'yan jam'iyar PDP sun koma APC | isyaku.com

  Fiye da mutum 25,000 yan jam'iyar PDP karkashin jagorancin Alh.Bello Doya da wasu manya manyan mukarrabai a cikin jam'iyar PDP sun canja sheka zuwa jam'iyar APC wanda ya sami albarkar Gwamna Akiku Bagudu,manya manyan shugabannin jam'iyar APC da daruruwan jama'a daga kananan hukumomi 21 da ke fadin jhar.

  Manya daga cikin yan jam'iyar ta PDP da suka koma APC ranar Lahadi sun hada da Ambassada Isah Argungu,da 'yan majalisar dokoki na jihar Kebbi su uku 'yan jam'iyar PDP karkashin jagorancin Muhammed Ismail,tsofaffin Chiyaman na kananan hukumomi su goma da sauran jama'a .

  Shugaban jam'iyar APC na jiha Alh.Attahiru Maccido ya tabbatar cewa mutanen sun canja sheka ne a bisa ra'ayin kansu.

  A nashi jawabin,Gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu ya shaida wa jama'a cewa zai tabbatar da adalci tsakanin tsofaffi da sababbin yan jam'iyar ta APC a fadin jihar.


   
  @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka aiko mana rahotu ? ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kebbi: Mutum 25.000 'yan jam'iyar PDP sun koma APC | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama