DSS ta kama mutum 5 da suka saci yaro dan shekara 7 a Katsina | isyaku.com

Hukumar tattara bayanai da ayyukan sirri da aka fi sani da jami'an tsaro na farin kaya watau DSS ta kama wasu mutane da take zargi da hannu wajen sace wani yaro a jihar Katsina inda ta gabatar da su a gaban wani Kotun Majistare a garin Katsina.

Wadanda ake zargin sun hada da Aisha Nasiru, 50,Habiba Nasiru,24,Ahmad Muhammad 20,Mustapha Abdullahi 20, Auwal Nura 20.Dukkannin mutanen an gabatar da su a gaban Kotu a bisa zargin hada baki don a sace yaron a yayin da yake dawowa daga makaranta a watan Nuwamba 2016.

Mai gabatar da kara A.H Al-sadiq ya shaida wa Kotu cewa mutanen sun aikata laifin ne a garin Funtua na jihar ta Katsina.

Mai shari'a  Mr.Nuraddeen El-ladan ya daga shari'ar zuwa ranar 13 ga watan Juli,yayin da ya ba da umarni a tsare wadanda ake tuhuma a gidan yari kafin wannan lokacin.

@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a SMS zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari.
DSS ta kama mutum 5 da suka saci yaro dan shekara 7 a Katsina | isyaku.com DSS ta kama mutum 5 da suka saci yaro dan shekara 7 a Katsina | isyaku.com Reviewed by on June 15, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.