An kashe wata mata da duka a bisa zargin maita | isyaku.com

Kwamishinan yansanda na jihar Adamawa Mr Moses Jitoboh ya tabbatar wa manema labairai  cewa wata mata 'yar shekara 32 ta sha duka daga hannun wasu mutane har sai da ta mutu.

Lamarin ya faru ne bayan kauyawan garin sun zargi matar da Maita da kuma kasancewa wadda take janyo rashe-rashen rayuka, rashin lafiya, da sauran matsalolin rayuwa a kauyen na Falu

Hukumar yansanda na jihar Adamawa ta kama wasu mutane da ake zargi da hannu a lamarin wanda ya hada da Abraham Adamu, 18, Malachi Yilafane, 35, Thomas Aji, 54, Zakariya Chorum, 56 da Miss Newana Ilihal, 20.
@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka aiko mana rahotu ? ka tuntube mu a birninkebbi080@gmail.com
An kashe wata mata da duka a bisa zargin maita | isyaku.com An kashe wata mata da duka a bisa zargin maita | isyaku.com Reviewed by on June 03, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.