• Labaran yau

  May 26, 2017

  Yadda Pastor ya damfari Titi Atiku Abubakar Naira Miliyan 918 | isyaku.com

  Uwagidan Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, ta bukaci babbar kotun shari’a da ke Legas, ta taimaka ta kwato mata hakkin ta a hannun wani fasto da ya ci amanar ta a kan naira miliyan 918 ta ba shi a matsayin za su yi kasuwanci.

  Titi Abubakar, ta ce tun farko ta yi tunani, kuma ta yi amanna cewa a matsayin sa na fasto ba zai cuce ta ko ya zambace ta ba.

  Rahotanni sun ce Titi ta bayyana wa kotun haka ne, a lokacin da ake yi mata tambayoyi dangane da abin da ta sani a kan tuhumar da ake yi wa Fasto Nsikak Abasi Akpan-Jacobs, da Abdulmaliki Ibrahim da kuma kamfanin Dana Motors, Ltd.

  Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ce ta gurfanar da wadanda ake tuhumar, inda ake zargin su da cin amana, zamba da kuma sata da kuma yi wa dukiyar wani babakere a kan naira miliyan 918, mallakar kamfanin THA Shipping Maritime Services Ltd, na matar Atiku.

  Yanzu haka dai, an sanya 5 da 6 ga watan Yuli a matsayin ranakun da za sake zama domin ci-gaba da sauraren shari’ar.


  @isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb

  Wannan labarin ya fara bayyana a shafin Liberty.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yadda Pastor ya damfari Titi Atiku Abubakar Naira Miliyan 918 | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama