• Labaran yau

  May 10, 2017

  Maiyama: An taimaka wa wadanda ibtila'in ruwan sama ya shafa

  Hukumar bayar da agaji na gaggawa ta Najeriya NEMA ta bayar da kayakin agaji ga wadanda suka rasa muhallin su sakamakon ruwan sama da aka yi makon da ya gabata a Garin Maiyama na karamar hukumar Maiyama da ke cikin jihar Kebbi.

  Jami'in hukumar NEMA sashen hulda da jama'a Sani Datti ya fadi haka ranar Talata a yayin da yake gabatar da kayakin ga Gwamna Atiku Abubakar Bagudu wanda shugaban hukumar na kasa Engr. Mustapha Yunusa Maihaja ya bayar.

  Kayakin sun hada da buhu 200 na shikafa ,200 na masara,200 na wake sai kuma bargo 300,gidan sauro 300,fallen silin 300,katifa 300,buhun siminti 300,fallayen kwanon rufin gida 300,pakiti 50 na kusa,da kuma wasu pakiti 30.

  Idan baku manta ba ,fiye da mutum 1000 lamarin ya shafa inda ruwan sama da matsanancin iska ya janyo rasa muhalli  ta hanyar kwashe rufin gidaje,rusa wasu gidaje,Makarantu da wasu ababen more rayuwa.

  @isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Maiyama: An taimaka wa wadanda ibtila'in ruwan sama ya shafa Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama