Mako biyu kenan shugaba Buhari bai sami zuwa Sallar Juma'a ba

Rahotanni da ke fitowa daga Abuja sun tabbatar cewa shugaba Muhammadu Buhari bai sami halartar sallar Juma'a ba a Masallacin Fadar shugaban kasa inda aka saba ganin sa domin yin Sallah tare da manyan jami'an Gwamnatin sa da kuma wasu Gwamnoni makonni biyu da suka gabata.

Yan Najeriya nata cece kuce game da rashin lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari a yayin da ya rage bayyana a cikin jama'a tun bayan da ya dawo daga hutu a kasar Ingila inda Likitoci suka duba lafiyar sa.Buhari dai ya shafe makonni biyu kenan bai halarci taron zartarwa ba a fadar ta shugaban kasa.

A wata sanarwa da ya fitar a jiya,Babban mai ba shugaban kasa shawara kan harkar labarai Garba Shehu,ya ce rashin bayyanar shugaba Buhari a bainar jama'a da wasu hidima da ya shafi kasa ba wai yana nufin shugaban baya da lafiya bane.Ya kara da cewa Likitoci sun shawarci shugaba Buhari ya dinga samun hutu.


@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb


Mako biyu kenan shugaba Buhari bai sami zuwa Sallar Juma'a ba Mako biyu kenan shugaba Buhari bai sami zuwa Sallar Juma'a ba Reviewed by on April 28, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.