EFCC ta daukaka kara,ta bukaci a dakatar da aiwatar da hukuncin Kotu akan Patience Jonathan

Rahotanni da muka samu sun nuna cewa matar tsohon shugaban kasar Najeriya Mr.Goodluck Jonathan watau Dame Patience Jonathan ta ziyarci Bankin Skyebank da ke unguwar Maitama domin ta wawuri kudade daga cikin dala miliyan 5.9 da wata Kotu a jihar Lagos ta bayar da umarni a sake mata asusun ajiyarta.

Amma a yayin da take cikin Bankin,Madam Patience ta fuskanci cikas a yayin da taci karo da cewa jami'an hukumar EFCC sun shigar da kara domin a dakatar da aiwatar da hukuncin da Kotu a jihar Lagos ta bayar a ranar 6 ga watan Afrilu,bugu da kari  hukumar ta EFCC ta daukaka kara akan hukuncin da Kotun ta yanke akan zancen na asusun Madam Patience Jonathan.

Kamfanin dillancin labarai ta Najeriya NAN,ta ruwaito cewa rahotanni da ba'a tabbatar da sahihancin su ba sun nuna cewa Madam Patience ta je Bankin ranar Juma'a 7/4/2017 inda ta bukaci ta zare dala miliyan daya amma sai mahukuntar Bankin suka bata dala 100,000.

NAN ta ci gaba ta cewa Madam Patience ta sake dawowa da karfe goma na safe inda ta tattauna da manajan Bankin da misalin karfe 10:00 na safe.Daga karshe ta bar Bankin da karfe 4:05 na yamma kuma bata ce wa kowa uffan ba a yayin da ta fito daga Bankin.

@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb
EFCC ta daukaka kara,ta bukaci a dakatar da aiwatar da hukuncin Kotu akan Patience Jonathan EFCC ta daukaka kara,ta bukaci a dakatar da aiwatar da hukuncin Kotu akan Patience Jonathan Reviewed by on April 10, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.