Civil Defence ta dakatar da jami'an ta 2 akan zargin satar mai

Hukumar tsaro ta Civil Defence, ta dakatar da wasu jami’an ta 2 daga aiki, bisa zargin su da hannu a satar wasu albarkatun man fetur a jihar Bayelsa.

Mai Magana da yawun rundunar Emmanuel Okeh ya sanar da haka a wata zantawa da ya yi da manema labarai a Abuja.

Ya ce hukumar ta yi Allah-wadai da zargin da ake yi wa jami’an nata da mallakar albarkatun man fetur ba bisa ka’ida ba.

Wannan dai ya na zuwa ne bayan rundunar ‘yan sanda ta gabatar da mutanen 2 ga manema labarai bayan ta kama su da laifin.

Emmanuel, ya ce tuni kwamandan rundunar Abdullahi Muhammadu ya kafa kwamitin da zai gudanar da bincike, tare da hukunta jami’an kamar yadda dokar hukumar ta tanada.

Wadanda aka Kama da laifin kuwa sun hada da mataimakin Sufritanda Agah Utavie, da kuma Angel Kilosomewo, inda aka dakatar da su har sai an kammala bincike.

Liberty

@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb
Civil Defence ta dakatar da jami'an ta 2 akan zargin satar mai Civil Defence ta dakatar da jami'an ta 2 akan zargin satar mai Reviewed by on April 03, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.