• Labaran yau

  March 21, 2017

  Malaman Firamare 2 sun yi wa dalibar su fyade


  Rundunar 'yan sanda ta jihar Bauchi tana zargin wasu Malaman makarantar firamare 'yan shekaru 33 da 39 da yi wa wata Yarinya 'yar firamare fyade wannan lamarin ya faru ne a unguwan Dutsen Tashi da ke jahar Bauchi.


  Ana zargin malaman ne akan cewa sun kai yarinyar wani waje ne inda suka aikata wannan danyen aikin,rahotanni sun nuna cewa yarinyar dalibar su ce.

  Kwamishinan 'yan sanda na jihar Bauchi Garba Baba Umar ya nuna matukar bakin ciki akan faruwar wannan lamarin,ya kuma sha alwashin gabatar da duk mai irin wannan halin gaban kuliya domin su fuskanci hukunci.

  @isyakuweb -Ku biyo mu a Facebook
  https://web.facebook.com/isyakuweb
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Malaman Firamare 2 sun yi wa dalibar su fyade Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama