Kotun Adamawa ta daure tsohon gwamnan jihar Bala Ngilari

Wata kotu a Adamawa dake Najeriya ta yankewa tsohon Gwamnan Jihar, Bala James Ngilari hukuncin daurin shekaru 5 a gidan yari saboda sa...


Wata kotu a Adamawa dake Najeriya ta yankewa tsohon Gwamnan Jihar, Bala James Ngilari hukuncin daurin shekaru 5 a gidan yari saboda samun sa da laifin karya dokar bayar da kwangila.
Alkalin kotun Nathan Musa, yace ya gamsu da shaidun da aka gabatar masa dangane da zargin da ake yiwa tsohon gwamnan, inda ya bada umurnin daure shi na shekaru biyar ba tare da zabin biyan tara ba.
Sai dai alkalin kotun ya bai wa Ngillari zabin gidan yarin da yake so a aiwatar masa da hukuncin.
Hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin Najeriya EFCC ce tagurfanar da tsohon gwamnan tare da Sakataren gwamnatinsa Ibrahim Weyle, sai kuma kwamishinan kudinsa Sanda Lamurde, bisa laifin sabawa dokokin bada kwangilar sayan motoci kirar Hilux kan kudi naira miliyan 167.8 a lokacin da suke bakin aiki.
To sai dai kuma kotun ta wanke sauran mutane biyun, yayinda ta yankewa tsohon gwamna, bala Ngilari hukuncin na shekaru 5 a gidan yari.
Ngilari ya kasance mataimakin gwamna ga yayin mulkin tsohon gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako tsawon shekaru 7, har zuwa lokacin da aka tsige Nyako a watan July na shekara ta 2014.

RFI

COMMENTS

Name

AL-AJABI,25,BIDIYO,1,BIRNIN-KEBBI,26,DUNIYA,23,FADAKARWA,23,FASAHA,3,HOTUNA,41,JAKAR MAGORI,20,LABARI,426,NISHADI,51,SANARWA,13,SHARHI,13,SIYASA,17,TARIHI,7,WASANNI,8,
ltr
item
ISYAKU.COM: Kotun Adamawa ta daure tsohon gwamnan jihar Bala Ngilari
Kotun Adamawa ta daure tsohon gwamnan jihar Bala Ngilari
https://4.bp.blogspot.com/-Zq8AzIWEiI8/WL2k6qjgqXI/AAAAAAAADX4/61GM_wgMWv8504nqf6v7SLAJa_YdTzy8QCLcB/s320/Ngilari_1.jpg
https://4.bp.blogspot.com/-Zq8AzIWEiI8/WL2k6qjgqXI/AAAAAAAADX4/61GM_wgMWv8504nqf6v7SLAJa_YdTzy8QCLcB/s72-c/Ngilari_1.jpg
ISYAKU.COM
http://www.isyaku.com/2017/03/kotun-adamawa-ta-daure-tsohon-gwamnan.html
http://www.isyaku.com/
http://www.isyaku.com/
http://www.isyaku.com/2017/03/kotun-adamawa-ta-daure-tsohon-gwamnan.html
true
3052478943858316060
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts KARANTA SAURAN LABARAI Karanta saura Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All KARANTA WADANNAN LABEL MAADANI BINCIKA GABADAYAN LABARAI Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS CONTENT IS PREMIUM Please share to unlock Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy