Gwamna Atiku Bagudu |
A bisa wannan labarin isyaku.com ta kaddamar da bincike akan
wannan zargi wanda tuni ya haifar da jite-jite da babu ma’ana balle kyau ga lissafin
saurare.Binciken dai ya nuna cewa,bayan da aka kammala wannan Addu’ar ne,aka
bukaci wadanda suka shirya wannan taron su je gidan Gwamnati inda mai girma
Gwamnan jihar Kebbi ya yi umarni akan cewa aba su Naira Miliyan biyu.Amma da
yake lokacin Juma’a ya gabato domin ranar Juma’a ne,sai aka fara bayar da Naira
Miliyan daya wanda ake zargin sun fado a hannun wani Malam Adamu,kuma aka raba kudin a tsakanin dukkannin wadanda suke da hannu a wajen shirya wannan taron na Addu'a nan take.
A bisa wannan tsarin ne majiyar tamu ta gano cewa,an sami
matsin lamba daga sauran mutane da ke cikin wadanda suka shirya wannan taron ne
akan cewa ala tilas sai dai a raba wannan Miliyan daya da aka bayar,saboda su
ne suka fara shigowa hannu.A bisa wannan fahimta tsakanin bangaren Malam Adamu
da bangaren wani Muhammed Bello Abubakar sai aka raba kudin tare da manufar
cewa idan an bayar da cikon Miliyan daya sai a fitar da kaso na Sadaka don Malamai da
wadanda abin ya shafa.
Majiyar tamu ta kara da cewa,Muhammed Bello Abubakar ya karbo
cikon sauran kudin ,watau miliyan daya daga bisani,amma bai zo ba balle a ci
gaba da lissafin da aka faro tun farko a bisa fahimta balle a ware wa
Malamai kason nasu da sauran wadanda abin ya shafa.Bayanai sun nuna cewa sauran
cikon miliyan daya yana wajen Muhammed Bello Abubakar.A ci gaba da tantance
gaskiyar lamarin,isyaku.com ta lalabo lambar wayar salula ta Muhammed Bello
Abubakar domin ta samu korafin sa game da lamarin amma wayar salular sa a kashe
take tun yammaci jiya har yanzu da aka rubuta wannan rahotun.
Alaramma Ibrahim Bayawa |
A yayin da isyaku.com ta tuntubi shugaban hadaddar kungiyar
Malami da Limamai ta jihar kebbi Alaramma Ibrahim Bayawa,ya yi bayani akan cewa su kam basu san da zancen ba, amma suna jin rade-raden cewa za'a ba Malamai Miliyan daya na Sadaka,amma har ya zuwa yau 1/3/2017
basu gan ko kwabo ba.Ya kuma roki Malamai da aka gaiyato su suka baro abin da
suke yi,kuma suka zo suka gudanar da wannan Addu’ar don Allah da cewa su yi
hakuri,ya kuma kara da cewa ai dama ba domin a ba su wani abu ne suka yi Addu’ar
ba illa don Allah.
Binciken namu ya nuna cewa an gaiyato akalla Malamai 15 wasu
ma daga kananan hukumomi ne wanda ya hade rinjayen kungiyoyin Addinin Musulunci
da ke cikin jihar Kebbi,amma kuma sai ga wannan lamari ramas dadin ji ya
faru.…to me ke faruwa ne a jihar mu ta Kebbi?.Ku karanta labaran da
isyaku.com ta bayar akan Addu’ar ranar 23/2/2017 da na ranar Juma’a 24/2/2017.
Isyaku Garba – Birnin kebbi @isyakuweb Ku biyo mu a Facebook