Bataliyar Sojin Birnin kebbi sun yi wasan karshen Shekara

Bataliyar soji ta Daya 1st Battalion da ke garin Birnin Kebbi ta gudanar da bikin karshen shakara ta 2016,kamfanin dillancin Najeriya NAN ta rubuto cewa bukukuwan da aka sa wa suna WASA an gudanar da shi ne domin murnar nassara akan ayyukan horo da tsare- tsare a shekarar da ta gabata.
Bikin dai ya sami wakilcin Maimartaba Sarkin Gwandu wanda Galidiman Gwandu Alh.Ibrahim Bashar yayi.
A yayin bikin an gudanar da wasan Daba (Durbar) na dawaki da raye-raye daga Mata da Yaran Sojojin,'Yan bautar kasa ta NYSC da dai sauran kade-kade.
Bataliyar Sojin Birnin kebbi sun yi wasan karshen Shekara Bataliyar Sojin Birnin kebbi sun yi wasan karshen Shekara Reviewed by on February 06, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.