AN HANA SOJIN NAJERIYA WALLAFA HOTUNA A INTANET

An hana sojojin Najeriya wallafa hotuna ko bidiyon ayyukansu a shafukan sada zumunta.
Wannan mataki ya biyo bayan fitar wani faifan bidiyo ne a kwanakin baya, inda aka nuna wasu sojoji suna korafin karancin abinci da sauran kayan aiki.
Sojojin dai na cikin wata runduna ne da ke yakar kungiyar Boko Haram a Arewa maso Gabashin kasar.
A wani jawabi da ya gabatar a madadin Shugaban rundunar sojin kasar Tukur Buratai a birnin Kaduna, Manjo-Janar Adeniyi Oyebade ya yi kira ga sojojin da su yi taka-tsan-tsan.
"Ina gargadin ku kan amfani da shafukan sada zumunta a lokacin da kuke cikin aiki.
Za ku iya jin kuna bukatar daukar hotunan abokan aikinku masu kyau, amma ku yi taka-tsan-tsan wurin yin hakan," in ji shi.
Ya kara da cewa "ku kau cewa wallafa duk wani hoto ko bidiyo wanda ya shafi abokan aikinku ko kuma aikin naku kai tsaye".
Ana yawan yada hotuna da bidiyon dakarun Najeriya musamman wadanda ke fagen dagar yaki da Boko Haram.
BBC HAUSA

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN