• Labaran yau

  December 08, 2016

  SABON SHAFIN YANAR GIZO NA DAKARKARI DA MUTANEN ZURU NA JIHAR KEBBI

  Al'ummar kasar Zuru musamman Dakarkari da aka sani da taimakon juna,aiki tukuru,gaskiya da rikon amana sun sami wani bawan Allah a cikin su da ya habaka,kuma ya yunkura inda ya tsara kuma ya samar da wannan shafin yanar gizon
  da aka sa ma adireshin yanar gizo na zuruonline.com 
  Tuni dai wannan shafin ya fara aiki wanda ke samar da labarai da harshen turanci saboda samar da daidaita tsakanin mutanen na kasar Zuru wajen fahimtar ainihin sakon da ake son gabatarwa ga al'ummar kasar ta Zuru ta wannan shafin,wanda ya hada da sanarwa,ilmantarwa da kuma samar da labaran kasar Zuru.
  Masu jagorancin wannan shafin suna tuntubar manyan 'yan kasar ta Zuru kan yanda za'a tsara tafiyar da shafin,ciki wayan da aka rubuta wa takarda har da Mai Martaba Sarkin Zuru Alh.Dr.Sani Sami Gomo2 da mai girma mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi Alh.Samaila Dabai Yombe.Wannan abin koyi ne ga sauran al'umma.

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: SABON SHAFIN YANAR GIZO NA DAKARKARI DA MUTANEN ZURU NA JIHAR KEBBI Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama