• Labaran yau

  December 02, 2016

  GWAMNA DA DAN MAJALISA SUN YI DAMBE   Wasu gagga-gaggan shahararrun yan siya, kuma shuwagabannin al’ummar sun dambace yayin gudanar da yakin neman zabe, inda suka dinga kai ma juna naushi, tokari da hantara.
  Wannan lamari ya faru ne a kasar Kenya yayin da jam’iyyar ‘Orange Democratic Movement Party’ (ODMP) taje yakin neman zabe a wanni yankin kasar, inda Gwamna Cyprian Awiti da dan majalisa Oyugi Magwanga, wakilin jama’a Kasipu-Kabondo suka dambace sakamakon cacar baki data shiga tsakaninsu.
  Wannan abin kunya ya faru ne a gaban dubun dubatar mutane, da kyar tsohon shugaban kasa Raila Odinga ya samu daman raba su.Damben nasu ya kai dambe tunda har sai da suka kai juna kasa. Rikicin dai ya samu asali ne lokacin da wasu magoya bayan gwamna Awiti ke kirar ya kamata a kara zaben gwamnan a zabukan 2017, amma kuma a dawo da Magwanga saboda a cewar su bai tabuka komai ba a majalisa.

  Daga Muhammad Auwal naij.com

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: GWAMNA DA DAN MAJALISA SUN YI DAMBE Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama