• Labaran yau

  November 14, 2016

  NCC ZATA CI MTN DA SAURAN KAMFANONIN SADARWA NA WAYAN SALULA TARA

  Hukumar da ke sa ido don ganin an tabbatar da bin ka'ida kan kamfanonin sadarwa na salula NCC ta ba kamfanonin wayar salula na Najeriya wa'adin mako daya da su bi ka'idar da ta dora masu na daina aika sakonnin tallace- tallace na ba gaira ba dalili da wasu kamfanonin ke yi musamman MTN.

  Tuni dai NCC ta umarci kamfanonin da su fito da tsarin daina takura wa kostoma ta hanyar ba shi kostoman zabi ko yana son ya dinga samun sakon tallace tallace da kamfunan sadarwar ko baya so, ta hanyar zabin DND watau do not disturb.Amma bisa ga dukkan alama wasu daga cikin kamfanonin basu cika wannan ka'idan umarnin ba.


  Daga cikin kamfunan da umarnin ya shafa dai sun hada da  Airtel Network Ltd., MTN Nigeria, Globacom Nigeria, Smile Communication, Visafone Communications, Ntel, Etisalat, Multi links, Starcomms, Danjay Telecoms, Gamjitel Ltd. da Gicell wireless.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: NCC ZATA CI MTN DA SAURAN KAMFANONIN SADARWA NA WAYAN SALULA TARA Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama