• Labaran yau

  November 27, 2016

  BA'A YABON DAN KUTURU

  Wani mutum ne yayi sabuwar amarya sai abokanshi suka gamu da shi suka ce masa ya amarya, sai yace kai aini ana cewa mata tara suke basu cika goma ba amma ni matata ta cika goma cif,
  dan matata “muslimatin, muminatin, kanitatin, sadikatin, sa’imatin kai har zuwa wa’abukara. Sai suka ce kai amma kayi sa’a, Allah ya bada zaman lafiya.
  Bayan kwana kadan sai suka hadu da abokansa, sai suka ce masa ya muslimatun? sai yace ai yanxu ta zama”muguwatun,munafukatun, kazamiyatun, makiratin, shegiyatin, azzalumatin.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: BA'A YABON DAN KUTURU Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama