• Labaran yau

  October 25, 2016

  Matasan jihar Kebbi su dinga bincika cabinet office domin samun bayanai game da ayyukan gwamnati

  Yazid M.Shehu
  Daraktan ayyukkan musamman da kulawa (director careers and counselling) na cabinet office Birnin kebbi Malam Yazid M.Shehu ya bukaci matasan jihar Kebbi da cewa su dinga bincika cabinet office lokaci zuwa lokaci domin sanin dama da ake da shi a gwamnatance na daukan ma'aikta a ma'aikatun gwamnatin Najeriya saboda 'yan jihar Kebbi su sami wadataccen wakilci a duk sassan ayyukan gwamnatin tarayya.

  Malam Yazid ya kuma bukaci matasa,maza da mata yan jihar kebbi masu neman ayyukan gwamnatin jihar Kebbi da na tarayya da su dinga bincika isyaku.com tun da yanzu ta shiga cikin jerin hanyar sadarwar sanar da jama'a cikin sauki ta hanyar yanan gizo da cabinet office ke yi.
   
  isyaku.com dai shafi ne na Isyaka Seniora wanda aka gina shi don amfanin jama'ar jihar Kebbi.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Matasan jihar Kebbi su dinga bincika cabinet office domin samun bayanai game da ayyukan gwamnati Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama