An gano daya daga cikin wajajen da ake sayar da jarirai

Sashe na binciken ayyukan kungiyoyin asiri na hukumar 'yan sanda na jihar Rivers ta kai samame inda ta gano inda ake harkar sayar da jarirai a karamar hukumar Etche na jihar Rivers,yayin da aka kama wani Reginald Akagbuto da wasu 'yan mata masu ciki su hudu 'yan kasa da shekaru 20.

Ayayin bincike na 'yansanda 'yan matan sun shaida wa 'yansanda cewa shi uban gidan nasu Akagbuto shi ke taimaka wajen saida masu da jariran bayan sun haihu,na miji dai ana sayar da shi akan kudi naira N150.000 ita mace kuma naira N100.000.Hukumar 'yansandan jihar Rivers dai na ci gaba da bincike
An gano daya daga cikin wajajen da ake sayar da jarirai An gano daya daga cikin wajajen da ake sayar da jarirai Reviewed by Isyaku Garba on October 21, 2016 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

Powered by Blogger.