Isyaku Garba Zuru

Na buda wannan shafin ne domin samar da labarai musamman na Jihar Kebbi da arewacin Najeriya ta hanyar yanar gizo. Domin kuma mu ba talaka mai karamin karfi damar isar da sakonsa a jaridance a wajen da talaka bai iya kaiwa ga manyan jaridu. Gaskiyar lamari shine Mujallar ISYAKU.COM ya sami isa ga miliyoyin masu karatu a gida da kasashen Duniya wanda suka hada da kasar Amurka, Jamus, Pakistan, Libya, Japan, India, Germany, Norway, Spain watau Andalus, Canada, Kenya, Uganda, Jamhuriyar Niger, Sudan, Cameroun, Central African Republic, Jamhuriyar Benin, Egypt watau Masar, Saudi Arebia, da uwa gida Najeriya.

Sa'ilin da labarai na gida jihar Kebbi basu samu ba sai mu samo labarai na Nishadantarwa kamar labaran Al'ajabi,Fadakarwa ko Nishadantarwa, sharhi da fashin baki kan al'amurran yau da kullum wadanda su ne muka fi bayar da karfi a kan su, domin bincike da muka yi ya nuna cewa irin wadannan labaran ne jama'ar kasar Hausa suka fi karantawa.

Ni Isyaku Garba Zuru, dan asalin kasar Zuru a Masarautar Zuru da ke kudancin jihar Kebbi , Marubuci, Masani harkar ingizon wayar salula da sadarwar zamani, Manazarci akan harkar tsaro, 'dan jaridar zamani, kuma Mawallafi..Na yi karatun harkar Jarida ta yanar gizo daga cibiyoyi da dama.

Na kuma samar da sashen Turanci na Mujallarmu watau SENIORA POST, wanda za a iya samu a adireshin yanar gizo www.seniorapost.com wanda ke dauke da labaran turanci zalla.

ISYAKU.COM yana da ma'aikata da ke aiki karkashinsa guda uku, da wakilai hudu a fadin jihar Kebbi kawo yanzu.

Muna maraba da ku a ko da yaushe.

MUN GODE.