Yahaya Bello: Sanata ya yi maganar yiwuwar tsige Ganduje daga shugabancin APC


Tsohon Sanatan gabashin Kogi, Alex Kadiri ya caccaki magoya bayan Yahaya Bello da ke nema masa wuri a APC NWC.

Vanguard ta rahoto Sanata Alex Kadiri yana mai bayyana rade-radin tsige Abdullahi Umar Ganduje a matsayin abin babban dariya. Legit ya wallafa.

Dan siyasar yana ganin masu huro wuta a kori shugaban APC na kasa domin kawo Yahaya Bello, makiyan jam’iyya mai-ci ne.

Kadiri ya zargi masu kiran da yakar APC ta cikin gida kokarin ganin bayan jam’iyyar lokacin da fastocin Bello suka fara yawa a Abuja.

Dattijon wanda yana cikin iyayen APC musamman a jihar Kogi ya yi tir da rikon da Yahaya Bello ya yi na shekaru har takwas a ofis.

Sanata Kadiri wanda ya wakilci Kogi a majalisar dattawa tsakanin 1999 da 2003 ya ce APC ta kawo masu ci baya a mulkin Bello.

Duk abin da yake faruwa, ‘dan siyasar ya ce bai damu da gwamnatin Bola Tinubu ba, yake cewa halin jihar Kogi ne kawai gabansa.

“Alex Kadiri bai kwadayin mukami. Na yi Darekta Janar, na zama Sanata, shugaban majalisar kula da jami’a da babban sakatare,"

"Mai kuma zan nema da Ubangiji bai yi mani ba?"

- Alex Kadiri

An rahoto Kadiri yana zargin Yahaya Bello da cin mutuncin Ata Igala da Sanata mai-ci kafin ya sauka saboda yana rike da mulki.

An rahoto Kadiri yana zargin Yahaya Bello da cin mutuncin Ata Igala da Sanata mai-ci kafin ya sauka saboda yana rike da mulki.

Ba mu da kima ne? Yanzu fastocin tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello sun cika Abuja, yana so ya canji Ganduje."

"Ta ya za mu burma daga wannan gazawa zuwa wannan?"

- Alex Kadiri

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN